Isa ga babban shafi
Canada-Afghanistan

Sojin Canada sun kawo karshen aiki a Afghanistan

Kasar Canada ta sanar a hukumance cewa ta kawo karshen aikin da sojojinta ke yi a Afghanistan karkashin inuwar kungiyar tsaro ta NATO bayan share tsawon shekaru 12 a cikin kasar.

Sojojin Kungiyar tsaro ta NATO a Afghanistan
Sojojin Kungiyar tsaro ta NATO a Afghanistan REUTERS/Mohammad Ismail
Talla

Kimanin sojoji 40,000 ne daga kasar Canada suka gudanar da ayyukan yaki da Mayakan Taliban da kuma Al Qaeda a cikin shekaru 12 a Afganistan.

A shekarar 2001 ne kasar Canada ta aika da dakarunta zuwa Afghanistan har zuwa 2011
A cikin wata sanarwa daga ma’aikatan tsaro, gwamnatin Canada tace tana alfahari da agajin da ta kai wa Afghanistan. Amma akwai Sojojin kasar kimanin 160 da suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.