Isa ga babban shafi
Ukraine

Poroshenko ya lashe zaben Ukraine

Hukumar dake kula da zabe a kasar Ukraine ta bayyana cewa Petro Poroshenko ya lashe zaben shugaban kasar da aka ka yi a ranar lahadin da ta gabata, wanda zabe ne mai matukar muhimmanci a tarihin kasar. Hukumar ta bayyana hakan ne bayan da ta ce ya samu sama da rabin kuri'un da aka kada. 

Petro Porochenko, mutumin da ya lashe zaben kasar Ukraine
Petro Porochenko, mutumin da ya lashe zaben kasar Ukraine REUTERS/David Mdzinarishvili
Talla

Kasar ta Ukraine ta gudanar da zaben ne yayin da tashin hankalin da ake fama da shi a gabashin kasar ke ci gaba da kazanta.

“A yanzu zamu iya tabbatar da cewa, babu bukatar a je zabe a zagaye na biyu, a ranar 25 ga watan Mayu na shekarar 2014, an zabi sabon shugaban kasar a Ukraine.” Shugaban hukumar zaben kasar Mykhailo Okhendovskyi ya gayawa ‘yan jarida.

Tuni dai kasashen duniya suka fara bayyana ra’ayoyinsu game da wannan sakamakon zabe inda Sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya sha alwashin za su mara sabon shugaban baya.

Tun kamin a bayyana Poroshenko a matsayin mutumin da ya lashe zaben kasar, ya bayyana cewa ba zai amince ‘yan awaren kasar su ci gaba da tayar da hankula mutanen kasar ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.