Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Rasha ta ce zai yi wuya a gudanar da zaben shugabacin kasar Ukraine

Rasha ta bayyana shakkunta a game da yiyuwar gudanar da zaben shugaban kasar Ukraine a ranar 25 ga wannan wata na Mayu, a daidai lokacin da ake gwabza fada tsakanin sojan gwamnati da kuma ‘yan aware a yankuna da dama na kasar.

Sojan Ukraine a yankin Slaviansk
Sojan Ukraine a yankin Slaviansk REUTERS/Yannis Behrakis
Talla

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta fitar a wannan asabar na cewa ‘’yanayin da kasar ke ciki, ba zai bayar da damar gudanar da zabe akan tafarki irin na dimokuradiyya ba’’.

Yanzu haka dai dakarun gwamnatin Ukraine na ci gaba da gwabza fada da ‘yan aware da aka ce na samun goyon baya ne daga Rasha a lardunan Slavyansk da kuma Donestsk, inda aka samu asarar rayukan mutane da dama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.