Isa ga babban shafi
Amurka-Afghanistan

Amurka ta sako 'yan Taliba 5 ta karbi sojan ta daya

Jiya Asabar aka sako wani sojan Amurka da aka kama fiye da shekaru 5 a kasar Afghanistan, a matsayin musaya, da wasu ‘yan Taliban da Amurkan ke tsare dasu a gidan yarin Guantanamo. Hukumomin kasar ta Qatar ne suka shiga tsakani wajen kulla yarjejeniyar musayar, data ‘yanta Saje Bowe Bergdahl, lamarin daya dauki hankulan duniya.Sai dai tuni wasu suka fara sukar wannan musayar, inda dan majalisar Dattijan Amurka na jama’iyyar Republican John McCain, da yayi marhabun da sako sojan kasar, ya bayyana ‘yan Taliban din da aka sako a matsayin kangararru.Yau Lahadi ‘yan kasar Afghanistan sun yi ta farin ciki, sakamamkon musayar sojan Amurka da ‘yan Taliban 5, da ke tsare a gidan yarin Guantanamo na kasar ta Amurka.Wata sanarwar da kungiyar ta Taliban ta fitar, ta bayyana Mohammad Fazl, Norullah Noori, Mohammed Nabi, Khairullah Khairkhwa da Abdul Haq Wasiq a matsayin sunaye mutane da aka sako.Ita ma ma’aikatar harkokin wajen Amurkan ta tabbatar da sunayen mutanen, da a halin yanzu suke a kasar Qatar.  

Saje Bowe Bergdahl, da 'yan Taliban suka sako a maimakon 'yan kungiyar su 5
Saje Bowe Bergdahl, da 'yan Taliban suka sako a maimakon 'yan kungiyar su 5 AFP PHOTO HANDOUT-INTELCENTER"
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.