Isa ga babban shafi
Iraqi-Amurka

Amurka ta yi watsi da bukatar Kurdawan Iraqi

Kasar Amurka ta yi watsi da bukatar da shugaban gwamnatin cin gashin kai ta Kudurwan kasar Iraki Massud Barzani ya gabatar wa majalisar dokokin yankin Kurdistan, inda ya bukaci a amince a shirya kuri’ar jin ra’ayin jama’a domin ballewar yankin daga kasar baki daya.

Shugaban Kurdawa Massoud Barzani yana ganawa da Sakataren harakokin wajen Amurka john Kerry
Shugaban Kurdawa Massoud Barzani yana ganawa da Sakataren harakokin wajen Amurka john Kerry REUTERS/Stringer
Talla

Mai Magana da yawun fadar Amurka ta White House Joseph Earnest, ya ce babu yadda Iraqi za ta iya tunkarar Mayakan jihadi face idan kasar na hade.

Firaministan Iraqi Nuri al-Maliki ya yi tayin afuwa ga Mayakan da suka karbe ikon wasu biranen kasar, tare da yin watsi da bukatar Barzani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.