Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinawa

Isra’ila da Hamas suna ci gaba da luguden wuta

Kimanin Mutane 22 aka ruwaito sun mutu a hare haren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa a zirin Gaza a rana ta biyar a yau Assabar, yayin da kuma Hamas ke ci gaba da cilla rokoki zuwa yankunan Isra’ila. Tony Blair wanda ke wakiltar Majalisar Dinkin duniya da kungiyar Tarayyar Turai da Amurka da Rasha ya isa kasar Masar domin tattaunawa da mahukuntan kasar akan yadda za’a shawo kan rikicin Gabas ta tsakiya.

Wani Bafalasdine a kusa da wani wuri da ke cin wuta inda 'Yan sanda suka ce ya faru ne sakamakon hare haren da Isra'ila ke kai wa a Gaza.
Wani Bafalasdine a kusa da wani wuri da ke cin wuta inda 'Yan sanda suka ce ya faru ne sakamakon hare haren da Isra'ila ke kai wa a Gaza. REUTERS/Ashraf Amrah
Talla

Dukkanin bangarorin biyu sun yi watsi da kiran tsagaita wuta da manyan kasashen duniya suka yi.

Rahotanni sun ce Isra’ila ta fara jibge dakarunta da tankokin yaki a kusa da Gaza a wani mataki da ake ganin shiri ne na mamaye Gaza.

Jimillar Falasdinawa 127 aka ruwaito sun mutu a hare haren da Isra’ila ta kai a Gaza tun a ranar Talata.

Rundunar Sojin Isra’ila tace Hamas ta harba rokoki 530 zuwa cikin Isra’ila, kuma a yau Assabar an cilla rokoki guda Tara.

Isra’ila ta kaddamar da yaki ne akan kungiyar Hamas a Gaza, tun bayan sacewa da kashe wasu Yahudawa guda uku da wani matashin Bafalasdine da aka kona da ransa.

A ranar Litinin ne Ministocin harakokin wajen kasashen Larabawa suka ce zasu gana a birnin al Kahira domin tattauna batun rikicin Isra’ila da Falasdinawa da ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.