Isa ga babban shafi
Ecuador

An kama wani nau'in hadar ibilis ta ruwa a kasar Ecuador

Jami’an gwamnatin kasar Ecuador sun cafke ton 7.8, na kayan maye na ruwa, da ake kyautata zaton wani nau’in hodar ibilis ne, da ake shirin kaiwa kasar Spain. Yayin samamen na garin Guayaquil, da ke gabar ruwan kudu maso gabashin kasar ta Ecuador, jami’an tsaro sun kama wasu mutane 3, da ake zargin suna da hannu a lamarin, kuma tuni aka tusa keyar su zuwa gidan kaso.Hukumomi sun ce masu neman wucewa da sinadarin sun nuna kama maganin wanke cutuka ne, amma sai bincike ya gamo cewa wani nau’in cocaine ne, da ake kira hydrochloride. 

Shugaban kasar Ecuador, Rafael Correa
Shugaban kasar Ecuador, Rafael Correa Guillermo Granja
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.