Isa ga babban shafi
NATO

Taron Kungiyar NATO a Birtaniya

Shugabannin Kungiyar tsaro ta NATO za su gudanar da taro a Birtaniya inda ake sa ran zasu dauki mataki akan Rasha game da rikicin Ukraine, bayan Faransa ta bayyana dakatar da huldar tsakanin da Rasha. Rikicin Ukraine da barazanar Mayakan IS a Iraqi da Syria ana ganin su ne muhimman batutuwan da da zasu mamaye zaman taton na kwanaki biyu da za a gudanar a birnin Newport a Wales.

Taron Kungiyar tsaro ta NATO/OTAN a Wales
Taron Kungiyar tsaro ta NATO/OTAN a Wales REUTERS/Yves Herman
Talla

Shugaban NATO Anders Fogh Rasmussen yace Rasha babbar barazana ce a rikicin Ukraine. Shugaban Amurka Barack Obama da Firaministan Birtaniya David Cameron sun ce zasu hade wa Rasha kai domin ba Ukraine goyon baya.

Wannan taron shi ne na farko da kungiyar NATO za ta gudanar tun bayan na shekara ta 2012 a birnin Chicago a Amurka sannan karo na farko a Birtaniya tun wanda aka gudanar a shekara ta 1990.

Rikicin kasar Ukraine da Rasha ke da hannu wajen ballewar yankin Crimea wani batu ne da NATO zata mayar da hankali ganin yadda al’amarin ke ci gaba da janyo hasarar rayuka da dukiya.

Siyasar kasar Afghanistan da kuma yadda kungiyar NATO zata fito da wasu dabaru na kare kasashe membobinta daga hare haren kungiyoyin ta’adda na daga cikin batutuwan da taron zai duba a yayin da ake sa ido domin ganin yadda taron na bana zai kara tabbatar da yadda kungiyar ke kokarin karfafa dangantakarta a sassa daban daban domin tabbatar da zaman lafiya da zai kai ga bunkasar tattalin arzikin duniya

NATO tace tana da tabbas cewa idan har aka hada kai tsakanin al’umomin duniya, to batun nasara akan barazanar tashin hankulan da duniya ke fuskanta yanzu a hannun ‘Yan ta’adda mai yiyuwa ne

Akalla kasashe 40 daga sassan duniya ne suke cikin wannan kawancen na NATO.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.