Faransa
Hollande yana ziyara a Canada
Shugaba Francois Hollande na Faransa ya isa kasar Canada a yau Lahadi, a wata ziyarar kwanaki uku da ya kai a kasar domin tattauna batun inganta huldar kasuwanci da tsaro tsakanin manyan kasashen na duniya guda biyu.
Wallafawa ranar:
Talla
Hollande shi ne shugaban Faransa na farko da ya kai ziyarar kasar Canada, tun zamanin Francois Mitterand a shekara ta 1987.‘
Yan kasuwar Faransa kimanin 40 ne suka raki shugaban, wanda zai jagoranci tattaunawar kasuwanci tsakaninsu da ‘Yan kasuwar kasar Canada.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu