Isa ga babban shafi
Amurka

Republican ta lashe zaben Majalisar Dattijai

Jam’iyyar Republican a Amurka ta lashe akasarin kujerun Majalisar Dattawan kasar a zaben da aka gudanar jiya abin da zai ba Jam’iyyar damar karbe ikon Majalisar. Tuni shugaba Barack Obama ya danganta zaben a matsayin zakaran gwajin dafi ga zaben 2016.

Dan Republican Scott Walker yana murnar lashe zaben Amurka a Milwoukee Wisconsin
Dan Republican Scott Walker yana murnar lashe zaben Amurka a Milwoukee Wisconsin REUTERS/Sara Stathas
Talla

Republican ta lashe kujeru a Iowa da Monatana da Colarado da Arkansar da North Carolina da West Virginia da South Dakota a zaben wanda ake gudanarwa duk abayn shekaru biyu a Amurka.

Lashe kujerun Jihohin North Carolina da Iowa ya bai wa Jam’iyar Republican Karin kujerun Majalisar dattawa bakwai da ta ke nema don samun akalla kujeru 52 na Majalisar mai kujeru 100 domin jagorancinta.

Rahotanni kuma sun ce yanzu haka Jam’iyar na hanyar lashe wasu Karin kujeru a Majalisar wakilai wanda dama ita ke da rinjaye.

Tashar talabijin na CBS ta yi hasashen cewar Jam’iyar Republican na iya samun kujeru 245 daga Majalisar mai kujeru 435.

Masu sa ido a harkokin siyasa na kallon wannan zaben a matsayin wani zakaran gwajin dafi kan yadda zaben shugaban kasar zai kaya a shekarar 2016.

Shugaba Obama na Democrat yace wannan zaben shi zai auna farin jininsa. Wannan nasarar ta Jam’iyar Republican na iya kawo tarnaki wajen aiwatar da manufofin shugaba Barack Obama na Democrat.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.