Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

An saki Bafaransar da aka sace a Afrika ta tsakiya

Ministan Harakokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius ya tabbatar da cewa an saki Jami’ar agaji Bafaransa da Mayakan anti-balaka suka sace a kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya. Amma mahukuntan na Faransa ba  su bayyana yadda aka saki Claudia Priest ba.

Sojojin da ke fada da Mayakan Balaka a Afrika ta tsakiya
Sojojin da ke fada da Mayakan Balaka a Afrika ta tsakiya REUTERS/Siegfried Modola
Talla

A ranar Litinin ne aka sake Priest mai shekaru 67 tare da wani dan kasar Afrika ta tsakiya a birnin Bangui.

Ana danganta sace Jami’an agaji a matsayin martani da Mayakan balaka suka mayar bayan cafke wasu shugabanninsu a karshen makon da ya gabata.

Mayakan Balaka dai Kiristoci ne da ke fada da Mayakan Seleka Musulmi a kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya, tun bayan da Seleka ta karbe ikon gwamnati a watan Maris din 2013.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.