Isa ga babban shafi
Faransa-Masar

Faransa da Masar sun kulla cinikin jiragen yaki

Kasar Faransa ta kulla cinikin sayarwa da Masar jiragen saman yaki 24 da ake kira Rafale Fighter Jets akan kudi kusan Dala biliyan 6. Ministan tsaron Faransa Jean Yves Le Drian da shugaban kasar Abdel Fatah al Sisi suka sanya ido wajen sanya hannu kan yarjejeniyar a birnin al Kahira.

Ministan tsaron Faransa  Jean-Yves Le Drian tare da Abdel Fattah al-Sissi a birnin Al Kahira
Ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian tare da Abdel Fattah al-Sissi a birnin Al Kahira
Talla

Ministan tsaron Masar Sedki Sobhi ya ce jiragen za su taimakawa kasar wajen fuskantar duk wani kalubalen da ke gabanta musamman bazaranar mayakan IS da suka yi wa wasu Kiristocin kasar yankan rago a Libya.

Faransa ta yi alkawalin ba Masar Jiragen kafin karshen shekarar nan kamar yadda suka amince a yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.