Amurka ta sake yin alkawalin lada akan ISIS
Kasar Amurka ta sake sanar da diyyar miliyoyin daloli kan duk wanda zai tsegunta ma ta inda za ta samu labari akan shugabanin kungiyar mayakan ISIS. Sanarwar da ma’aikatar tsaron Amurka ta bayar jiya ya bayyana sunayen shugabanin kungiyar ISIL 4 a matsayin wadanda Amurka ke nema ruwa a jallo.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sunayen sun hada da Abdel Rahman Mustafa al Qaduli, wanda aka sanya Dala miliyan 7 akansa, sai kuma Abu Muhammad al Adnani, Dan kasar Syria wanda aka sanya Dala miliyan 5 akansa, saboda yadda ya ke ta kiran cewar a kai wa Amurka hari.
Sauran sun hada da Tarkhan Batirashivli, wanda aka fi sani da Omar al Shishani, wanda aka sanya Dala miliyan 5 akan sa da kuma Tariq bin al Tahar bin al Falih al Awni al Harzi, dan kasar Tunisia, wanda ake zargi da tara kudaden da kungiyar ke aiki da su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu