Isa ga babban shafi
Canada

Wani mutum ya kashe iyalansa saboda diyar shi tana fa da ciwon kai

‘Yan sandan kasar Canada suna bincike kan yadda wani mutum ya kashe diyar shi da matar da kuma ‘yar uwar shi, kafin ya kone kanshi. Mutumin mai sun Randy Janzen, ya rubuta a shifin sada zumunta na Facebook cewa ya kashe diyar tashi mai shekaru 19 ne, saboda ta shafe rayuwarta tana fama da wani irin ciwon kai mai tsanani da ake kiramigraines, dake sata dimaucewa.Ya kuma ce ya kashe matar shi saboda a cewar shi, bai kamata a baiwa uwa labarin mutuwar diyarta ba, yayin da kuma yace ya kamata ‘yar uwar tashi ta leka barzahu, sabo aika aikar da yayi zata jefa ta a kunya.Ganin sanarwar da Janzen ya sanya a Facebook, sai ‘yan sanda suka bazama neman shi, amma kuma ya shiga wani gida ya cinna wuta a lokacin da yake ciki har ya mutu. 

Alamar gangamin hana kisan kai a Faransa
Alamar gangamin hana kisan kai a Faransa @AQPS
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.