Isa ga babban shafi
Amurka-Arabs

Obama na fukantar jan aiki wajen gamsar da Sarakuna yankin Gulf

Shugaban kasar Amurka Barack Obama, na fuskantar Jan aiki, wajen gamsar da kasashen larabawa yankin Gulf a game da sassanta matsalolin da ke tsakanin kasashen da Amurka.Wannan dai na zuwa ne a taron yini biyu da Obama ya gayyace shugabanin da sarkunan yankin Gulf domin tattauna hanyar sassanta duk wata matsala da ke tsakanin su.

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Shugabannin kasashe Larabawa yankin Gulf shida ne dai Shugaba Barack Obama ya gayyata fadar tasa domin warware dukkan matsalolin da ke tsakanin su

Taron da aka gudanar a fadar white house kana aka nufi Camp David na cike da cece-kuce, ganin sarakuna biyu kadai wato na Kuwait da Qatar, ne daga cikin shida na yankin Gulf suka hallarci taron.

Rikicin kasar Yemen na daga cikin batutuwa da aka mayar da hankali akai, kuma Amurka ta bukaci kulla kyakyawar hulda tsakanin su, duk da dai a yanzu, ana cikin wani yanayi mai tatare da kalubali lura da abubuwa da ke faruwa a gabas ta tsakiya

Kasashen yankin Gulf dai na bukatar Amurka ta tabbar masu da cewa, Iran ba zata zama barazana agaresu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.