Isa ga babban shafi
Isra'ila

Matsalar Iran ta fi IS illa-Netanyahu

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya yi gargadi ga kasashen Duniya cewa, barin Iran ta mallaki makamin nukiliya abu ne da ya fi kungiyar ISIL muni fiye da sau dubu. Netanyahu ya ce kungiyar ISIS barazana ce, amma ya danganta Iran a matsayin kasar ‘yan ta’adda.

Firiya Minista Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firiya Minista Isra'ila Benjamin Netanyahu REUTERS/Ronen Zvulun
Talla

Netanyahu ya ce matukar Iran ta mallaki makamin nukiliya za ta fi Kungiyar IS da ke da’awar Jihadi mugunta fiye da sau dubu.

Kalaman shugaban na Yahudawa na zuwa ne a yayin da kwararru daga bangaren Iran da manyan kasashen duniya ke shirin ganawa a Vienna kafin cikar wa’adin cim ma yarjejeniyar nukiliyar a ranar 30 ga watan Yuni.

Netanyahu ya dade yana adawa da sasantawar da kasashen Amurka da birtaniya da Faransa da Rasha da Jamus ke yi da Iran don cim ma yarjejeniya da ita akan yadda zata dakatar da shirinta na Nukiliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.