Isa ga babban shafi
Faransa-Iraqi-syria

Yaki da kungiyar Isis, Dukar Taiki ne ana barin Jaki

Shugaban rundunar sojan kasar Faransa, Janar Denis Mercier, ya yi kiran kasashen kawance dake yakar kungiyar mujahidan islama a Syriya da Iraki da su ci gaba da kai hare hare a kan sansanonin mayakan kungiyar ISIS dake ci gaba da haifar da zaman zullumi  a duniya.

jiragen yakin kasar Fransa a sararin samaniyar Iraki
jiragen yakin kasar Fransa a sararin samaniyar Iraki AFP / JEAN-LUC BRUNET
Talla

A wata fira da manema labarai a jiya, mai matsayin farko a jerin rundunar sojan kasar Fransa Janar Denis Mercier ya ce, idan aka dauki misali da kasar Libiya sun kaddamar da hare harensu ne a kan ruhin matsalar itace shugaba Kaddafi, wanda hakan ne ya basu damar kawar da shi, ba wai sun yi ta kai hare haren bane a cikin iska

Sai dai misalin ya sha bambam da abinda ke faruwa a kasashen Iraki da Syriya, inda ake yawan kai hare haren ne a fagen daga, amma ba inda ya dace ba, kan kungiyar ta ISIS, a kasar ta Iraki kamar yadda yake a Syriya

Janar Mercier ya kara da cewa, a kasar Syriya inda Fransa bata cikin jerin masu kai hare hare, rundunar hadakar kasashen duniya da Amruka ke jagoranta, na fuskantar tabarbarewar lamurra, domin kuwa a hareharen da dakarun kasashen duniya ke kaiwa a Syriya, ana fuskantar babbar barazanar kara karfafa gwamnatin Bashar Al Assad ne, a yayin da a Iraki, gwamnatin ta bukaci dakarun na duniyar kar su kai hare haren a inda ya dace a daki matsalar.

Janar Mercier ya dora Kalmar tambaya dangane da tasirin da hare haren jiragern saman da kasashen duniya ke yi wajen yakar kungiyar ta Isis, inda yace, ba don dakarun kashen duniya a kasar ba, da tuni kungiyar Majahidan dake kokarin kafa daular Islama a kasashen Iraki da Syriya ISIS, ta karbe madafan iko a ko ina cikin fadin kasar ta Iraki da ya hada da birnin Badaza babban birnin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.