Isa ga babban shafi
Iraqi-Amurka

Watakila mayakan ISIS su hana amfani da ruwan tafkin Ramadi na kasar Iraqi

Jamian Kasar Iraqi suna fara fargabar kungiyar ISIS masu da’awar kafa daular Islama suna iya amfani da azabtar da mazauna garin Ramadi wajen hana jama’a amfani da ruwa daga tafkin dake samarda ruwa a garin.Matakin na zuwa ne ganin yadda dakarun kasar ke kokarin dannawa garin na Ramadi, kwana daya bayan da Janar John Allen, Jagoran kawancen Amurka dake taro a Paris gameda dabarun yakar kungiyar ISIS, ke cewa yakar kungiyar ISIS na iya daukan lokaci mai tsawon gaske.Duk da nasarar da kungiyar ta ISIS ke samu na kwace wasu garuruwa a Iraqi da Syria, Amurka na cewa komi na tafiya daidai.Fraiministan Irakin Haider al-Abadi ya fadi ranar 17 ga watan Mayu bayan Kungiyar ISIS ta kwace garin Ramadi, wanda shine cibiyar Lardin Anbar, cewa Dakarun kasar zasu sake kwace garin.Yanzu haka dai Dakarun Iraqin na cewa mayakan ISIS sun rufe madatsar ruwa na Ramadi, kamar yadda Sabah Karhout, shugaban lardin ke cewa, kuma hakan zai galabaitar da yara, da mata da tsofaffi ta yadda kowa zai tsere ya barsu suyi yadda suke so. 

Fraiministan kasar Iraqi Haïdar al-Abadi tare da shugaban Amurka Barack Obama
Fraiministan kasar Iraqi Haïdar al-Abadi tare da shugaban Amurka Barack Obama REUTERS/Jonathan Ernst
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.