Isa ga babban shafi
Najeriya-Chadi

Boko Haram tana biyayya ga kungiyar ISIS

Shugaban kungiyar Abubakar shekau ya fidda wani sakon da a ciki yake bayyana biyayyar kungiyar tashi ga mayakan ISIL dake tayar da kayar baya a yankin gabas ta tsakiya. Cikin wani sautin da kungiyar ta sanya a shafinta na Twitter, Abubakar Shekau yace kungiyar ta Boko Haram tayi na’am da ayyukan kungiyar ta ISIL.Wannan Ikirarin na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun kasashen Niger da Chadi sun kaddamar da hare hare ta kasa da sama, kan mayakan kungiyar ta Boko Haram, a yankin arewa maso gabashin Nigeria.Dakarun suna kai hare haren ne, don kawo karshen mayakan na Boko Haram na zuwa ne bayan. Yanzu fiye da wata guda kenan da dubun dubatar sojoji suka ja daaga a yankin Diffa, inda suka yiwa ‘yan boko haram din kofar rago, don kawo karshe barazanar tsaron da suke yi a tsakanin kasashen yankin.Tashe tashen hankulan dake da alaka da kungiyar Boko Haram sun yi sanadiyyar rasa ran a kalla mutane dubu, yayinda wasu miliyon da rabi kuma suka tsere daga gidajensu, a kasashen Nigeria, Niger da Kamaru.A halin da ake ciki kuma, yau Litinin dakarun kasashen Niger da Chadi sun karbe garin Damasak na arewacin Nigeria daga hannun mayakan Boko Haram, bayan sun hallaka 'yan ta'adda da suka kai 200 yayin gumurzun da suka yi. 

Shugaban kungiyra Boko Haram, Abubakar Shekau.
Shugaban kungiyra Boko Haram, Abubakar Shekau. AFP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.