Duniya ta gaza wajen kare Yaran Syria- Malala
Malala Yousafzai, da ke gwagwarmayar tabbatar da ilimin ‘ya'ya mata da kare hakkin yara ta shaidawa shugabanin duniya cewar sun gaza wajen kare yaran kasar Syria da yaki ya daidaita.
Wallafawa ranar:
Malala da ke bikin cika shekaru 18 na haihuwa ta fadi haka ne a lokacin da ta ke bude wata makarantar Yara 200 da suka tserewa rikicin kasar Syria suka samu mafaka a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Lebanon.
Makarantar wadda ta mata ce kawai za ta horar da yaran ‘yan shekaru 14 zuwa 18.
Malala ta ce ta kawo ziyara ne a madadin yara sama da miliyan 28 da yaki ya raba da karatu.
‘Yan gudun hijirar Syria sama da Miliyan guda ke rayuwa a Lebanon.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu