Isa ga babban shafi
Amurka

An ruga da George W Bush zuwa Asibiti

Rahotanni daga kasar Amurka sun ce an ruga da tsohon shugaban kasar George W Bush asibiti bayan ya fadi a gidansa da ke Kennebunkport a Maine, ya kuma karya kashin wuyansa. Amma Mai Magana da yawun tsohon shugaban mai shekaru 91 Jim McGrath ya ce yana cikin yanayi mai kyau.

Tsohon Shugaban Amurka George H.W. Bush
Tsohon Shugaban Amurka George H.W. Bush AFP/Michael loccisano
Talla

MCgrath ya fadi a Twitter cewa suna fatar ganin an sallami tsohon shugaban ba tare da daukar dogon lokaci ba.

Rahotanni daga Amurka sun ce an kwashi tsohon shugaban na Amurka ne zuwa Asibitin Portland bayan ya kwanta da rashin lafiya a ranar Laraba.

Yanzu haka dai Bush na tafiya ne da keke guragu wanda shi ne tsohon shugaba mafi tsufa cikin tsoffin shugabannin Amurka guda hudu da ke raye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.