Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka za ta fara siyarwa kasashen larabawa makamai-Kerry

Bayan kammala tattaunawa da Wakilan kasashen larabawa kan batun kawar da duk wani shaku da ke akwai a kan yarjejeniyar shirin nukiliyar Iran, Sakataren kasahen wajen Amurka John Kerry ya ce za a hanzarta fara siyarwa kasashen larabawa yankin Gulf makamai. 

Sakataren kasashen wajen Amurka  John Kerry da Sarkin Qatar's Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani a fadarsa dake Doha
Sakataren kasashen wajen Amurka John Kerry da Sarkin Qatar's Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani a fadarsa dake Doha REUTERS/Brendan Smialowski/Pool
Talla

John Kerry wanda ke karkare ran gadi da ya ke yi a kasashen larabawa, ya bayyana haka ne a ganawar sa da Ministocin wajen kasashe shida da suka hada da na Bahrain da Kuwait, Oman, Saudiya da kuma Daular Larabawa.

Kerry Ya yi amfani da wannan dama ne dai, domin kawar da duk wani shakku a game da yarjejeniyar da manyan kasashen duniya suka cimma da kasar Iran na aikin nukiliyar ta da kuma mugun nufi da ake zargin Iran.

Bayan ganawar, Ministan wajen kasar Qatar Khalid Bin Mohammed Al-Attiyah ya ce cimma matsaya da Iran, itace ka dai mafi dacewa.

John Kerry ya kuma shaidawa manema labarai cewar sun cimma matsaya kan musayar bayyanan  sirri tsakanin Amurka da kasashen na Larabawa

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.