Isa ga babban shafi
Faransa

An fara nazarin gano jirgin malaysia da ya bace a Faransa

Masu bincike sun isa birnin Paris na kasar Faransa a yau litinin domin tattaunawa da hukumomin kasar a kan bacewar jirgin sama Malaysia samfurin MH370 da har yanzu babu duriyarsa sama da shekara guda.Lamarin da ke zuwa bayan gano wani bangare mai kama da na jirgin da akayi a karon farko a tekun La Reunion na kasar India.

REUTERS/Australian Defence Force/Handout
Talla

Tawagar Masu binciken karkashin Jagoranci daraktan sufurin jiragen sama kasar Malaysia Janar Azharuddin Abdul Rahman, za su fara tattaunawa da kwararun Faransa da jami’an ‘yan sanda kan hanyar da ya dace a bi wajen gano wannan jirgin sama da har yanzu babu labarinsa.

Sai dai a Wannan karon faransa ce za ta jagoranci bincike, bayan Hukumomi a kasar Malaysia sun gaskata bayanan da ke cewa sashen jirgin sama da aka gano a tsibirin La Reunion sannan kuma aka gudanar da bincike a kansa a kasar ta Faransa, ko shakka babu irin na jirgin kasar ta Malaysia ne da ya bata kimanin watanni 18 da suka gabata dauke da mutane 239 a cikinsa.

Tun bayan bacewar wannan jirgi, wannan ne karo na farko da aka gano wani abu da ya yi kama da irin nasa, lamarin da ake gani zai iya kara wa masu binciken kwarin gwiwa.

Daga ranar laraba mai zuwa ne kwararun kuma suka bayyana cewa za su gana da masana daga Kasar Amurka domin yin bincike mai tsanannin kan bangare jirgin da aka tsinto a tekun La Reunion lura da cewa ba a taba samun rahoton samun hatsarin jirgi a wannan yankin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.