Amurka
Clinton ta mayarwa da Bush martani
Hillary Clinton dake neman tsayawa takarar shugabancin Amurka karkashin jam’iyyar Democrat ta mayar da martini ga Jebb Bush na Republican kan kalamansa.
Wallafawa ranar:
Talla
A ranar talatar data gabata ne, Bush ya ce, janye dakarun soji da Amurka ta yi a Iraki a shekarar 2011 ya taimaka wajan baiwa Kungiyar ISIS gindin zama.
Har ila yau, Jebb Bush, ya caccaki gwamanatin Obama kan janye dakarun kuma tuni Clinton ta mayar masa da martini, inda tace, dan uwansa George Bush ne, ya cimma yarjejeniyar janye dakarun lokacin da yake rike da shugabancin Amurka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu