Isa ga babban shafi
Faransa-Najeriya

Hollande zai gayyaci Buhari taron Boko Haram

Shugaban Faransa Francois Hollande ya ce zai kira wani taro na musamman kan yadda za a magance rikicin Boko Haram da ke ci gaba da addabar kasashen da ke kewaye da tafkin Chadi.

Shugaban Faransa François Hollande, a fadarsa ta  Elysée a Paris.
Shugaban Faransa François Hollande, a fadarsa ta Elysée a Paris. REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Hollande ya fadi cikin jawabinsa ga Jami’an diflomasiya a yau Talata a Paris cewa nan da ‘yan kwanaki zai gayyaci Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da shugabannin kasashen da rikicin Boko Haram ya shafa zuwa taron duniya domin tattauna yadda za a kawo karshen kungiyar.

Hollande ya ce Faransa a shirye ta ke ta hada kan bangarorin da ke yaki da Boko Haram domin kawo karshen ayyukan kungiyar.

Boko Haram da ke addabar arewacin Najeriya tun a 2009 ta fadada hare harenta zuwa kasashen Nijar da Kamaru da Chadi. Kasashen kuma sun kafa runduna ta musamman domin murkushe ayyukan kungiyar.

Sai dai har yanzu rundunar mai dakaru 8,700 ba ta fara aiki gadan gadan ba akan Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.