Isa ga babban shafi
cuba

Paparoma ya bukaci a taimakawa Matalauta

Shugaban darikar katolika ta duniya, Paparoma Francis ya yi kira ga shugabanin darikar da su rungumi matalauta dake cikin halin kunci da kuma taimaka wa mutanen da aka manta da su. 

Shugaban darikar katolika ta duniya Paparoma Francis a lokacin da ya isa filin taron addu'ar a Cuba
Shugaban darikar katolika ta duniya Paparoma Francis a lokacin da ya isa filin taron addu'ar a Cuba 路透社
Talla

Yayin da ya ke jawabi ga dubban mabiyansa a Kasar Cuba, Paparoman ya ce arziki kan mayar da wasu mutanen matalauta matukar suka ki taimakawa wadanda basu da hali, saboda haka ya bukaci kai dauki ga marasa lafiya da wadanda aka manta da su.

Bayan taron addu’ar da ya jagoranta, Paparoman ya gana da tsohon shugaban kasar ta Cuba Fidel Castro mai shekaru 89 kuma sun tattauna kan batutuwa da dama da suka hada da muhalli kamar yadda mai Magana da yawun Fadar Vatican Federico Lombardi ya sanar.

Har ila yau, Paparoma ya baiwa Castro littatafai hudu kuma biyu daga cikinsu na ilimin  fahimtar addini ne.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.