Isa ga babban shafi
Afghanistan

NATO ta tura Dakarunta domin fada da Taliban

Kungigyar tsaro ta NATO ta bayyana cewa Dakarunta na musamman sun isa birnin Kunduz domin taimaka wa Sojojin Afghanistan wajan yakar Kungiyar Taliban da ta karbe ikon birnin Kunduz dake Arewacin Kasar.

Dakarun NATO na musamman da aka tura domin taimakawa Sojojin Afghanistan wajan yaki da Taliban
Dakarun NATO na musamman da aka tura domin taimakawa Sojojin Afghanistan wajan yaki da Taliban REUTERS/Stringer
Talla

Mai Magana da yawun NATO ya ce yaznu haka Dakarun na baiwa Sojojin Afghanistan shawarwari kan yadda za su bullowa Mayakan na Taliban.

Dakarun dai sun hada da na Kasashen Amurka da Birtaniya da Jamus yayin da kuma aka shiga rana ta uku ana gumurzu da Mayakan na Taliban da suka samu gagarumar nasara.

A dayan bangaren kuwa, Rahotanni sun ce Dakarun Amurka sun yi lugudan wuta kan Mayakan a cikin daren jiya yayin da zargin Taliban da dasa bama bamai a hanyoyin shiga birnin a dai dai lokacin da suke garkuwa da fararen hula a tsakanin su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.