Isa ga babban shafi
Faransa-China

Faransa da China sun cimma Yarjejeniyar rage tururin gurbata Muhalli

Shugaba Francois Hollande na Faransa ya kammala ziyarar aikin da ya kai a kasar China, inda kasashen biyu suka cimma jituwa dangane da batun rage tururin da ke gurbata muhalli, kafin taron kasashen duniya kan sauyin yanayi da za a fara a ranar 30 ga wannan wata na nuwamba a birnin Paris.

Shugaban Faransa Francois Hollande da takwaransa na China Xi Jinping
Shugaban Faransa Francois Hollande da takwaransa na China Xi Jinping REUTERS/Jason Lee/Pool
Talla

China, wadda a halin yanzu tafi kowace kasa fitar da hayakin da ke gurbata muhalli a duniya da kimanin kashi 25 cikin dari ita kadai, shugabanta Xi Jinping, a lokacin wannan ziyara ya tabbatar wa Francois Hollande cewa, kasar za ta bayar da hadin kadin-kai domin samun nasarar taron na birnin Paris.

Kafin wannan ganawa da shugabannin biyu suka yi, China, ta kasance daya daga cikin kasashen da suka ki amincewa da daftarin yarjejeniyar da ke tilastawa kowace kasa sauya dokokinta da suka shafi dumamayar yanayi a kowadanne shekaru biyar.

Firaministan China Li Keqiang, wanda ke gabatar da jawabi a lokacin da yake ganawa da Hollande, ya ce alhaki ya rataya a wuyan Sin, wajen samar da dokokin da za su taimaka wajen ragen dumamayar yanayi.

China dai ta ce kafin shekara ta 2030, za ta rage fitar da tururi mai gurbata yanayi da kimanin kashi 60 zuwa 65 cikin dari, wannan kuwa ta hanyar rage amfani da gawayi wajen samar da makamashin wutar lantarki domin kamfanoni da masana’antun kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.