Isa ga babban shafi
Amurka-

Obama na fatar gani an aiwatar da dokar takaita mallakar makamai a Amurka

Akalla mutane 14 wasu yan bindiga suka harbe har lahira a Carlifornia dake kasar Amurka kafin yan Sanda suka kashe 2 daga cikin maharan.Shugaban yan sandan San Bernardino Jarrod Burguan yace an gano wani da ake zargin yana daga cikin maharan da aka bayyana sunan sa a matsayin Syed Farook. 

Tutar Amurka
Tutar Amurka
Talla

Masana sun ce adadin mutane da yan bindiga suka kashe a cikin shekaru 12 a Amurka sun zarce wadanda aka kashe a yaki da wadanda cutar kanjamau AIDS ko Sida ta kashe.

Ranar 28 ga watan Novemba akalla mutane uku wani Dan bindiga ya kashe tare da kuma raunata wasu da dama bayan ya bude wuta a wata asibitin kula da kayyade iyali a Colorado a kasar ta  Amurka. Akwai Jami’in dan sanda cikin mutane uku da dan bindigar ya kashe.

An shafe lokaci ‘Yan sanda na musayar wuta da Maharin. Amma rahotanni sun ce Dan bindigar ya mika kansa a hannun ‘Yan sanda inda har yanzu ba san dalilin da ya sa ya kai harin ba.

Hukumomin Amurka sun bayyana sunan Dan bindigar a matsayin Robert Lewis dan asalin Carolina.

Shugaba Barack Obama ya sake bayyana cewar amincewa da dokar takaita mallakar makamai ce kawai zata magance yadda yan bindiga ke kashe mutane a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.