Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya yi hawaye saboda dokar mallakar makami a Amurka

Shugaban Amurka Barack Obama  cikin hawaye ya bukaci Amukawa su hukunta duk wani dan majalisa dake adawa da shirin takaita mallakar makamai a kasar ganin yadda ake amfani da su wajen hallaka jama'a.

Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Kewaye da wasu wadnda suka tsallake rijiya da baya a harin bindiga, Obama ya ce ana hallaka Amurkawa 30,000 a ko wace shekara ta hanyar amfani da bindigar.

Saboda wannan matsalar ce, ya sa  shugaba Obama ke neman yin amfani da karfin iko wanda kundin tsarin mulkin kasar ya ba shi domin daukar matakan da suka da ce na magance ta.

A jawabin da ya gabatar a birnin Washington, Obama ya ci gaba da cewa, bai kamata a zura ido gungun wasu mutane na ci gaba da yin garkuwa da Amurka ba, ma’ana hanawa kasar samar da dokokin da za su taikaita amfani da makamai a tsakanin al’umma.

Obama ya ce ta yaya za a mu ci gaba da zura ido ana kashe jama’a ba tare da wadanda alhakin kare rayuka ya rataya a wuyansu sun yi abinda ya dace ba.

Tun daga watan Disambar shekarar 2012, lokacin da wani dan bindiga ya bude wuta a makarantar Newtown da ke Connecticut har ya kashe yara 20 da kuma malamansu 6, Obama ke kokarin ganin an samar da dokoki da za su rage yaduwar makamai a hannayen jama’a amma abin ya gagara.

Jawabin nasa dai na a matsayin sako ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu ne daga matsalar yaduwar makamai a hannayen jama’a tsawon shekaru a Amurka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.