Isa ga babban shafi
Iran

Shugaba Rouhani na Iran na ziyara a Faransa

Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani ya kammala ziyara a Italiya a wannan laraba, inda ya isa Faransa domin ci gaba da ziyarsa ta farko a nahiyar Turai tun bayan da kasashen duniya suka janye takunkuman tatttalin arzikin da suka kakaba ma ta.

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani na ziyarar farko a nahiyar Turai tun bayan janye ma ta takunkuman tattalin arziki.
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani na ziyarar farko a nahiyar Turai tun bayan janye ma ta takunkuman tattalin arziki. REUTERS/President.ir/Handout
Talla

Ana sa ran shugaba Rouhani zai sanya hannu a yarjejeniyar cinikayya a ziyar da ya ke yi a birnin Paris na kasar Faransa, bayan yarjejenjiyar da ya cimma ta miliyoyin Dala a kasar Italiya.

Kasar Iran dai na bukatar siyan jiragen fasinja har guda 114 kirar Airbus domin inganta harkar sufurin jiragenta tare da maye gurbin tsoffin jirage da sabbi kuma ana sa ran tabbatar da wannan yarjejeniya a Faransa, yayin da kuma zai kulla hulda da kamfanonin kera motoci na Peugeot da Renault.

Shugaba Rouhani ya kammala ziyararsa ta kwanaki biyu a birnin Rome na Italiya, inda ya ziyarci gidan tarihi na Colosseum tare da ministan al’adu na kasar, Dario Franceschini da kuma tawagar ‘yan jarida.

Kana a karon farko, shugaban ya kai ziyara fadar Vatican, inda ya gana da shugaban mabiya darikar katolika na duniya Fafaroma Francis wanda ya bukaci Iran da ta taka rawa wajan samar da zaman lafiya a yankin gabas ta taskiya.

A lokacin da aka yi wa Rouhani tambaya kan cewa, ko Iran za ta bai wa Saudiya hakuri kan harin da ‘yan kasar suka kai ofishin jakadancinta a Tehran bayan kisan wani malamin shi’a a Saudiya Nimr al-Nimr, lamarin da ya yi sanadiyar tabarbarewar dangantaka tsakanin bangarorin biyu, sai shugaban ya ce, kasarsa ba ta shirya wani yunkurin neman sasantawa da Saudiyan ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.