Isa ga babban shafi
IRAN

Iran ta kama hanyar farfado da tattalin arzikin kasar

Shugaba Hassan Rouhani yau litinin ya soma ziyarar aiki a kasar Italiya, ziyararsa  ta farko bayan dagewa kasar takunkumin, wannan kuma  wani yunkurin ne na  farfado da dangataka a tsakanin Iran  da sauran kasashen duniya.

Shugaba  Rouhani tare da takwaransa  Sergio Mattarella na Italiya a birnin Roma
Shugaba Rouhani tare da takwaransa Sergio Mattarella na Italiya a birnin Roma Reuters/路透社
Talla

Shugaba Hassan Rouhani dake samun rakiyar ministoci da wasu manyan Yan kasuwar kasar akalla dari daya zai gana da Firaiyi minista Matteo Renzi a yammancin yau.

Iran na sa ran wannan tawagar dake marawa Rouhani baya za su taimaka wajen kulla yarjejeniya kasuwanci musanman batun siyan jiragen airbus da kasar ta saka a gaba.
A gobe talata ne ake sa ran Rouhani zai gana da Paparoma Francis a fadarsa ta Vatican sai kuma jibi laraba ya gana da shugaba Francois Hollande na Faransa, nan ma batun sabunta kwantiragin kanfanonin motocin Peugeot da Renault na daga cikin muhinman batutuwa da shugabanin biyu zasu fi mayar da hankali.

Tun a lokacin da Rouhani ya yi nasarar zama shugaban kasar Iran a shekara ta 2013 ya sha alwashin kawo karshen takunkumin da kasashen duniya suka kakkabawa kasar bisa dalilan tsarin nukiliyar kasar ya kuma ce zai yi duk iya mai yiyuwa na ganin ya sabunta dangata tsakanin Iran da sauran kasashen duniya.

Masu sharhi kan tattalin arziki a Iran na hasashen ganin kasar ta kulla yarjejeniyar kasuwanci da zai kai na kudi yuro biliyan 17 da kasar Italy kawai a wannan ziyarar
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.