Isa ga babban shafi
Iran

Takunkumi: Iran na jiran tsammani

Idan an jima a yau Asabar ake sa ran hukumar makamashi ta duniya IAEA zata sanar da cewa Iran ta cim ma bukatun yarjejeniyar da kasar ta kulla da manyan kasashen duniya kan dakatar da shirinta na nukiliya.

Ministan harakokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif
Ministan harakokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif Reuters
Talla

Yanzu haka ministan harakoin wajen Iran Mohammad Javad Zarif ya nufi Vienna domin tattaunawa da sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry da kuma babban jami’ar diflomasiyar Turai Federica Mogherini.

Bayan tattaunawar da zasu yi, ana sa ran bangarorin zasu sanar da cim ma bukatun yarjejeniyar da suka kulla a watan Yuli.

Matakin kuma zai sa kasashen Turai da amurka da Majalisar Dinkin Duniya su janye takunkuman da suka kakabawa Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.