Paparoma da Kirill na bukatar a kare lafiyar kiristoci
Shugaban darikar katolika ta duniya, Paparoma Francis da shugaban Kristocin Orthodox na Rasha Kirill, sun bukaci kasashen duniya da su kare lafiyar al’ummar Krista da ke fuskantar barazana a yankin gabas ta tsakiya.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugabanin dai na magana ne akan tashe tashen hankula da kungiyar ISIS ke haifarwa a gabas ta tsakiya.
Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar bayan ganawarsu mai cike da tarihi a Cuba, shugabanin sun ce, an lalata kauyuka da biranen mabiya addinin Kirista da dama a gabas ta tsakiya da arewacin Afrika tare da kaskanta wuraren ibadunsu.
Tuni dai Paparoma Francis ya isa kasar Mexico domin ci gaba da ziyarsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu