EU ta cimma yarjejeniya kan bukatar Birtaniya
Bayan shafe kwanaki biyu suna tattauna a birnin Brussels, shugabannin kasashen Turai sun cimma yarjejeniya kan bukatar Birtaniya na samar da sauye sauye a kungiyar tarayyar Turai, al’amarin da ya bude wa kasar kofar gudanar da kuri’ar raba gardama kan yiwuwar ci gaba da zamanta a kungiyar.
Wallafawa ranar:
Firaministan Birtaniya, David Cameron ya bayyana cewa, yarjejeniyar wadda aka cimma a cikin daren da ya gabata, za ta bai wa kasarsa matsayi na musamman kuma a yau Asabar ne zai gabatar da batun a gaban majalisar ministocinsa.
Mr. Cameron ya ce, zai yi kokarin shawo kan al-ummar Birataniya domin su amince da zama cikin kungiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu