Ana zaben Shugaban kasar Comoros yau Lahadi.
An bude rumfynan jefa kuriu a kasar Comoros inda al’ummar kasar ke zaben shugaban kasa yau lahadi.
Wallafawa ranar:
‘Yan takara 25 ke fafatawa a zaben da ake yi.
Bayanai na cewa tun da safe yau lahadi jama'a ke ta halartan wuraren jefa kuri'u domin tabbatar da ba’a bar su a baya ba.
Karkashin tsarin zaben kasar, mazauna yankin Grande Comore ne kawai za su jefa kuriun su, daga cikin yankuna uku da ake dasu, kamar yadda tsarin zaben kasar ya tanada.
‘Yan takara da suka yi nasara daga mazabun kasar uku ne zasu fafata domin fitar da wanda zai shugabanci kasar.
Kasar Tsubirin Comoros na da yawan mutane kasa da miliyan daya
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu