Isa ga babban shafi
EU-Turkiya

MDD na shakku kan yarjejeniyar ‘Yan gudun hijira

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare Hakkin Bil Adama sun bayyana cewar yarjejeniyar da kungiyar kasashen Turai ta kulla da kasar Turkiya na mayar da bakin da suka gudu daga Syria da Iraqi zuwa gida dan biyan Turkiya kudade ya saba ka’ida.

Dubban 'yan gudun hijira ke cikin wani hali akan iyakar Macedonia da Girka.
Dubban 'yan gudun hijira ke cikin wani hali akan iyakar Macedonia da Girka. REUTERS/Stoyan Nenov
Talla

Kwamishinan Yan gudun hijira na Majalisar Fillipo Grandi ya bayyana damuwar sa kan yadda kasashen zasu dauki matakin mayar da mutumin da ya gudu saboda yaki wata kasa ba tare da bashi kariya kamar yadda dokokin duniya suka tanadar ba.

Kungiyar Tarayyar Turai ta kulla yarjejeniyar ne da Turkiya domin rage kwararar ‘Yan gudun hijira da ke ci gaba da kokarin tsallakawa zuwa kasashen Turai.

Sai dai kuma ana bayyana shakku kan keta dokokin ‘Yan gudun hijira ta duniya game da batun mayar da bakin da suka tsallako daga Girka.

Karkashin yarjejeniyar, Turkiya ta amince ta karbi miliyoyan ‘Yan gudun hijirar Syria da Iraqi da suka tsallaka Turai daga Girka, a wani mataki da bangarorin biyu suka ce zai taimakawa wajen karya lagon ma su fataucin bakin ta kwale kwale.

Sai dai kuma yarjejeniyar ta cudanni in cude ka ce tsakanin Turkiya da Tarayya Turai kan ‘Yan gudun hijirar Syria.

Ga duk wani dan gudun hijirar Syria da Turkiya ta karba daga Girka, ita kuma Tarayyar Turai ta amince ta karbi Dan gudun hijira guda da ke rayuwa a sansaninsu da ke cikin Turkiya.

Wannan batun ne a yarjejeniyar ake ganin yana cike da rudani.

Wasu da suka bayyana adawa da tsarin, suna ganin za a keta dokin ‘yan gudun hijira ta duniya daga bangaren Turai musamman ganin Turkiya ba ta sanya hannu kan yarjejeniyar Geneva ba ta yan gudun hijira.

‘Yan Syria kusan Miliyan 3 ke rayuwa a sansaninsu a Turkiya, kuma a kullum dubun dubatar mutanen Syria da Iraqi ne kokarin tsallakawa zuwa kasashen Turai.

A yau Laraba hukumar Tarayyar Turai zata gabatar da sakamakon yarjejeniyar da ta kulla da Turkiya a zauren Majalisar kasashen a Brussels
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.