Isa ga babban shafi
Amurka

Zaben Amurka: Ana zaben fitar da gwani a jihohi 5

Ana gudanar da zaben fitar da gwani na Jam’iyyun siyasar Amurka guda biyu a jihohi biyar inda ‘yan takarar da ke kan gaba, Donald Trump na Republican da Hillary Clinton ta Democrat ke neman ci gaba da samun nasara fiye da sauran abokan takararsu a zaben na yau da ake kira Super Tuesday 2.

Donald Trump na Republican da Hillary Clinton ta Democrat
Donald Trump na Republican da Hillary Clinton ta Democrat REUTERS
Talla

Ana gudanar da zaben ne a Jihohin North Carolina da Ohio da Florida da Missouri da kuma Illinois.

Donald Trump na Republican da ke kan gaba a zabukan da aka gudanar a wasu jihohin Amurka a baya, a yau yana fatar samun gagarumar nasara don yin zarra ga sauran abokan takarar shi.

Ko da ya ke rikici da zanga-zanga da aka samu a gangamin yakin neman zaben Trumps a karshen mako shi ne ya mamaye kanun labaran Amurka, yayin da masu hammaya da shi a jam’iyyarsu ta Republican ke sukarsa.

A bangaren Democrat kuma ana ganin zaben na Super Tuesday na biyu zai kara ba Hillary Clinton tazara tsakaninta da babban mai hamayya da ita Bernie Sanders.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.