Isa ga babban shafi
China

China na kan bakarta ta baiwa Afrika dala biliyan 60

Kasar China ta ce, duk da tafiyar hawainiyar da tattalin arzikinta ke yi, ba za ta kauce daga kudirinta na baiwa nahiyar Afrika dala biliyan 60 don bunkasa yankin ba.

Shugaban kasar China  Xi Jinping da takwaransa na Zimbabwéen Robert Mugabe, da kuma na Afrika ta kudu Jacob Zuma.
Shugaban kasar China Xi Jinping da takwaransa na Zimbabwéen Robert Mugabe, da kuma na Afrika ta kudu Jacob Zuma. REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Duk da cewa dai kasar ta China za ta ci moriyar shirin sakamakon zuba jarin da kamfanoninta za su yi a nahiyar amma kasashen Afrika za su fi amfana da shirin saboda zai samar da dunbin ayyukan yi ga miliyoyin matasa, baya ga ci gaban da kamfanonin za su kawo a yankunan da aka kafa su kamar yadda ambasadan kasar ta China a Ethopia Li Yi Fan ya tabbatar.

A shekara ta 2015 ne dai tattalin arzikin China ya dan numfasa da kashi 6 da digo tara cikin 100, abinda ake gani tamkar tafiyar hawainiya idan aka kwatanta da na shekarun baya.

Shugaban kasar ta China Xi Jinping dai ya sanar da shirin bunkasa nahiyar Afrika da zai lakume makudan kudade, Inda ya ce, za a gina hanyoyi da bunkasa harkar noma da gina tashohin ruwa da layukan dogo na zamani, baya ga soke wasu basukan da kasar ke bin nahiyar.

Kasar China dai ta jima tana shawarwarin inda za ta zuba jari don bunkasa tattalin arzikinta amma yanzu ambasada Li ya ce, nahiyar Afrika ne ya dace da wannan kudiri.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.