Isa ga babban shafi
Vatican

Paparoma ya ce bai kamata a nunawa 'yan ci rani kyama ba

Jagoran mabiyar darikar Katolika Paparoma Francis, wanda ke gabatar da jawabi a hudubarsa dangane da zagayowar ranar Easter ko kuma Pâques da ya gabatar a wannan lahadi, ya bayyana damuwarsa a game da yadda kasashen Turai suka rufe iyakoki domin hana baki shiga a yankinsu.

Paparoma Francis
Paparoma Francis
Talla

Paparoma ya ce Yesu Almasihu ya koyar da mabiyansa nuna kauna a tsakanin juna musamman mutanen da suka tsincin kansu a cikin mawuyacin hali kamar yaki, yunwa, talauci da kuma rashin adalci.

Har ila yau Francis ya yi kakkausar suka a game da tsanantar ayyukan ta’addanci a duniya, yana mai cewa ya damu matuka a game da hare-hare na baya-bayan na da aka kai a kasashen Belgium, Turkiyya, Najeria, Chadi da kuma Cote d’Ivoire.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.