Isa ga babban shafi
Syria

Sojan Syria sun Gano Rami da Aka Birne Mutane 42 a yankin Palmyra

Sojan kasar Syria sun gano wani katon kabari da gawarwakin mutane akalla 42, fararen Hula da soja wadan da ake ganin kungiyar masu jihadi ta IS suka yi sanadiyyar ajalin su a yankin garin Palmyra.

Hasumiyar Palmyra ake hangowa nesabayan da sojan Bashar Assad suka saka kwato garin
Hasumiyar Palmyra ake hangowa nesabayan da sojan Bashar Assad suka saka kwato garin REUTERS/SANA/Handout via Reuters
Talla

Majiyoyin samun labarai sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa 24 daga cikin gawarwakin na fararen hula ne yayin da uku na kananan yara.

Majiyoyin na cewa an hallaka su ne ta hanyar yankan rago ko kuma harbi da bindiga.

An bayyana cewa yawancin gawarwakin an kai asibitin birnin Homs kuma har an gane wasu daga cikin mamatan.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama da wadan da dake sa idanu kan mamaye yankin Palmyra da ‘yan kungiyar IS suka yi na cewa cikin watanni 10 sun kashe mutane akalla 280.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.