Obama na son a maido da tsagaita wuta a Syria
Shugaban Amurka Barack Obama ya roki bangarorin da ke rikici da juna a Syria da su maido da yarjejeniyar tsagaita musayar wuta da suka cimma a baya, yayin da hare haren dakarun gwamnatin kasar da na ‘yan tawaye suka yi sanadiuyar mutuwar fafaren hula 26 a wannan Lahadi
Wallafawa ranar:
Makwanni takwas kenan da aka sanar da cimma wannan yarjejeniya amma rikici ya sake tsananta a kusa da yankin Aleppo, inda mutane ke rasa rayukansu sakamakon hare haren jiragen sama.
Obama wanda ke ziyara a Jamnus ya ce, ya zanta da takwaransa na Rasha, Vladmir Putin game da batun maido da zaman lafiya a Syria.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu