Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya bukaci mutunta dan adam a Vietnam

Shugaban Amurka Barack Obama ya fada wa gwamnatin kwaminisanci ta Vietnam cewa, mutunta hakkin dan adam ba zai haifar ma ta da barazana ba, abinda ake ganin tamkar yana bukatar gwamnatin da ta yi watsi da tsarinta na mulkin fir’aunanci.

Shugaban Amurka Barack Obama a birnin Hanoi na Vietnam
Shugaban Amurka Barack Obama a birnin Hanoi na Vietnam Reuters
Talla

Shugaban ya bayyana haka ne a jawabin daya gabatar a gaban al’ummar Vietnam a yau Talata a birnin Hanoi.

Gwamnatin Vietnam ta shahara wajen murkushe masu zanga zanga da kuma daure masu adawa da dokokinta a gidan yari.

Har ila yau gwamnatin ta yi fice wajen soke kungiyoyin kwadago, sannan kuma ita kadai ke cin karanta babu babbaka a kafafan yada labaran kasar.

Mr. Obama ya ce, kyautata hakkin dan adam wani mataki ne da ke tabbatar da zaman lafiya kuma abu ne da ke kawo ci gaba a kasa.

A karon farko kenan da Obama ya ziyarci Vietnam amma sau uku kenan da wani shugaban Amurka ya halarci kasar tun bayan yakin Vietnam da aka kawo karshensa a shekara ta1975.

Ziyarar Obama ta karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu, inda Amurka ta janye takunkumin siyar da makamai ga Vietnam tare da kulla yarjejeniyar kasuwanci da ita.

A bangare guda, shugaban na Amurka ya yi korafi kan yadda aka haramta wa wasu mambobin kungiyoyin fararen hula ganawa da shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.