Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta jibge 'yan sanda dubu 4 saboda Ingila da Rasha

Hukumomin Faransa na ci gaba da hana siyar da barasa a kusa da filayen da ake gudanar da wasannin gasar cin kofin Turai, yayin da suka yi shirin jibge karin jami’an ‘yan sanda dubu 4 a birnin Lille gabanin wasannin da Rasha da Ingila za su yi nan gaba.

Magoya bayan Rasha da Ingila sun yi gumurzu a Vieux-Port a Marseille na Faransa
Magoya bayan Rasha da Ingila sun yi gumurzu a Vieux-Port a Marseille na Faransa REUTERS/Jean-Paul Pelissier
Talla

Magoya banyan kasashen biyu duk sun taru a birnin na Lille domin wasan da Rasha za ta yi anjima da Slovakia da kuma wasan da Ingila za ta yi da Wales a gobe Alhamis.

Wannan ne ya sa ake dari darin cewa, da yiwuwar bangarorin biyu su kara yin arangama da juna baya ga wadda suka shafe kwanaki uku suna yi a birnin Marseille, abinda ya sa aka gurfanar da wasun su a kotu tare da yanke musu hukuncin dauri a gidan yari.

Gwamnatin Faransa ta ce, kwankwadon barasa na taimaka wa wajen tinzira magoya bayan har su tsindima cikin tashin hankali, kuma a yanzu haka an rufe shagunan siyar da barasar, sannan a yau a Laraba, za a rufe wuraren mashaya har guda 350 .
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.