Tarzoma ta barke a gasar Euro 2016
Wata sabuwar tarzoma ta barke tsakanin magoya bayan kasashe daban daban da suka taru domin gasar cin kofin Turai da Faransa ke daukan nauyi.
Wallafawa ranar:
Jami’an ‘yan sanda sun ce, rikicin ya barke ne a birnin Marseille da ke kudancin Faransa, kuma a dai dai lokacin da ake shirye shiryen fafatawa tsakanin Ingila da Rasha.
Tuni dai ‘yan sandan suka tarwatse masu hayaniyar da hayaki mai sa kwalla.
Idan anjima ne kuma, wasu mutane uku ‘yan asalin kasar Ingila da wata mata Bafaranshiya za su gurfana a gaban kotun Marseille kan zargin su ta tayar da tarzoma a lokacin gudanar da gasar ta EURO 2016.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu