Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta dauki matakai kan gasar Turai

Shugaban Faransa Francois Hollande ya ce, kasar ta dauki dukkanin matakan da suka wajaba domin tabbatar da sufurin jama’ar da suka je kasar domin gasar cin kofin kasashen Turai da kasar ke daukar nauyin gudanarwa tsawon wata daya daga yau juma’a.

Jami'an tsaro da ke sintiri a birnin Paris domin tabbatar da tsaro saboda gasar cin kofin Turai
Jami'an tsaro da ke sintiri a birnin Paris domin tabbatar da tsaro saboda gasar cin kofin Turai REUTERS/Charles Platiau
Talla

Har ila yau, an dauki tsauraran matakan tsaro don tabbatar da lafiyar dubban jama'ar, inda aka jibge jami'an tsaro kimanin dubu 90 saboda dari-darin yiwuwar kaddamar da harin ta'addanci a kasar wadda kungiyar IS ta kai wa munanan hare hare a bara tare da kashe mutane 130.

Mai masaukin baki da kanta ne wato Faransa, za ta bude fage da Romania a filin wasa na Stade De France da ke birnin Paris.

Sai dai filin wasan ya dan lalace sakamokon boren da kungiyar kwadago ta gudanar.

Tuni dai dubban ‘yan kallo daga sassan duniya musamman a nahiyar Turai suka isa Faransa domin gasar, inda a ka gudanar da gagarunmin biki a jajibirin wannan rana ta yau domin nuna farin ciki da fara gasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.