Kungiyoyin kwadago na yajin aiki a Faransa
Kungiyoyin Kwadago a kasar Faransa za su fadada yajin aikinsu zuwa bangaren jiragen kasa da sama a ci gaba da fafutukar ganin gwamnatin kasar ta sauya matsayinta kan dokar kwadago.
Wallafawa ranar:
Shirin shiga yajin aikin ya sa Firaminista Manuel Valls ya soke ziyarar aikin da ya shirya kai wa kasar Canada a tsakiyar watan gobe dominn fuskantar yajin aikin.
Wannan ita ce tafiya ta biyu da Valls ya soke saboda boren ma’aikata.
Ma’aikatan na adawa ne da sabbin dokokin kwadago da suka shafi kora da daukar ma’aikata cikin sauki.
Yajin aikin zai shafi ayyukan sufuri na jiragen kasa da sama, a yayin da ya rage mako biyu a soma gasar cin kofin nahiyar Turai a Faransa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu