Isa ga babban shafi
Faransa

Zanga-zangar Faransa na sake ta’azzara

An shiga rana ta 8 na zanga zangar kin amincewa da sabuwar dokar fasalta ayyukan kwadago a kasar Fransa, inda masu zanga zangar kungiyoyin kwadago da na dalibai tare da ‘yan farar hula ke ci gaba da datse hanyoyin shiga matatun kasar al’amarin da ya haifar da karancin man fetur a kasar.

Zanga-zangar adawa da tsarin kwadago a Faransa
Zanga-zangar adawa da tsarin kwadago a Faransa REUTERS/Charles Platiau
Talla

Baya ga wadanan masu zanga zangar, a yau sun sake karkata ga wasu sassan tattalin arzikin kasar domin hana ruwa gudu, a yau dai an yi dauki ba dadi tsakanin ‘yan sanda da masu zanga zangar dake rufe da fuskokinsu da suka baude daga jerin gwanon.

Friministan kasar Manuel Vals dai ya bayyana cewa babu gudu babu ja da baya sai dai wata kila za a iya yin ‘yan gyare gyare ga dokar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.