Isa ga babban shafi
Iran - France

Kamfanin Kera Motocin Peugeot-Citreon na Faransa na Shirin Komawa Iran

Kamfanin kera motocin Peugeot da Citreon na kasar Faransa ya sanar da shirin sake bude ofishin sa dake kasar Iran, inda har ya sanya hannu cikin yarjejeniyar aiki tare da Kamfanin Iran Khodro na kudi Euro miliyan 400. 

Shugaban kamfanin kera motocin Peugeot- Citreon PSA  Carlos Tavares
Shugaban kamfanin kera motocin Peugeot- Citreon PSA Carlos Tavares AFP PHOTO/Eric Piermont
Talla

A cikin watan biyu na shekara mai zuwa ne dai ake saran motocin farko da za'a kera karkashin yarjejeniyar zasu shiga kasar Iran kuma ana saran ganin an samar da motoci akalla dubu 200 duk shekara nan da shekaru biyu.

Jean Christophe Quemard mai kulada harkokin kamfanin Peugeot da Citreon a kasashen Tsakiya da Gabashin Africa ya fadi a lokacin sanya hannu cikin yarjejeniyar tsakanin kasashen biyu, a Tehran cewa wannan zumunci da Iran ya nuna a zahiri shaawar Kamfanin na zuba jari a Iran.

Ya fadi cewa kamfanin Peugeot Citreon na Faransa zai zuba jari ne na kudi Euro miliyan 400 cikin shekaru biyar.

A cewar Hashem Yekeh-Zareh, Shugaban Kamfanin Khodro na Iran wadanda aka kulla yarjejeniyar dasu kasha 30% na motocin da za'a kera zasu shiga  kasuwannin kasashen Gabas ta Tsakiya ne.

Kamfanin kera motocin na Peugeot Citreon na Faransa zai kasance na farko cikin kamfanonin kera motoci a Turai, da ya koma kasar Iran don harkokin sa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.