Faransa
Air France zai gurfanar da Ma'aikatansa
Hukumomin kamfanin jiragen sama na Air France sun ce za a gurfanar da wasu ma’aikatan kamfanin 5 a gaban kotu, saboda mummunar zanga zangar da suka yi wadda ta kai ga yaga rigar daya daga cikin manyan Daraktocin kamfanin.
Wallafawa ranar:
Talla
Wani binciken cikin gida da aka gudanar ya nuna cewar ma’aikata 10 suka jagoranci zanga zangar, amma biyar daga cikin su ake shirin gurfanarwa a gaban kotu.
Kamfanin na neman sauya dokar aiki ne da zai sanya matukan jiragen tafiyar karin sa’oi 100 a cikin kowacce shekara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu